[6:30pm, 11/7/2016] sadia tahir: *~SAFNAAH~*by billy tabaco~sad-nas
7......
da kyar ya kyaleta lokacin anfara kiraye-kirayen sallar farko,'lokacin bbu yadda take takai makura,wurin galabaita,'shikuwa murna yake yasamu banxa,'da kyar,ta kai kanta toilet,tayi kuka mai tsanani mai isarta,wandaya haddasa mata ciwon kai,"na janyo wa kaina dakaina,waiyyo ni shukrah!!.ta fashe da wani matsanancin kuka,"bayan kwana biyu cikin dare,taji motsi mutum,'tana bude ido taga kuku,'xatayi mgn ya nuna mata bindaga,dole ta rufe baki,ya gama biyan buqatarsa ya tsalleke sakarya."tun daga ranar kullum sai yaxo,sannan ya gargadeta idan ta fada ko ta rufe masa qofa,dai-dai da kwana daya saiya kasheta."bala'i ya ishi shukrah,ga wannan kuka,ta rame,ta lalace,ta fige kamar ba ita ba."hankalinta ya tashi lokacin da abdulrasheed yayo waya xai dawo gobe,kamar ta gudu takeji,'washe gari,tun da safe ya karayo wata wayar xai wuce germany,wani abun yataso,sai sati mai xuwa xai karaso,'ranar da xai iso kuwa,har guntun xawo ta ringa yi,wajen karfe goma ya'iso don haka tayi baccin karya,shikuwa bai sami kwanciya ba,sai wajen karfe uku,lokaci ya gama ganawa da ma'aikatan gidan,baiyi wani baccin kirki ba don ya rigata tashi,lokaci daya dawo daga masallaci sallar asuba,dai-dai ta fito daga toilet,gabansa ya fadi,'da sauri yace,ke kuwa bakida kirki!!! ta kalleshi a tsorace tace,menayi? "kinyi rashin lfy ne?"kinyi rashin lfy shine baxaki sanar dani ko a waya naturo likita ba,saikiyi shiru?wannan wace irin ramace haka kikayi?ta xura hijabi da sauri,tana fadin ae na warke,dan xaxxabi ne nayi,"wannan ta wuce da,saiki janyo min xagi a dangi da sauran mutan gari,"ya karasa mgn yana mai fita daga dakin,tare da kiran family doctor.
[6:30pm, 11/7/2016] sadia tahir: *~SAFNAAH~* by billy tabaco~sad-nas
8.......
"tagama sanya kaya kenan yashigo,"maxa ki fito likita xai duba ki,'saura kiris fitsari ya xubo mata,'simi-simi ta karasa,'ya gama yan gwaje-gwajensa wanda yakusan awa daya,sannan yace,'madam,kin iya shiga ciki,"meke damunta?ya buqata,'likitan ya dube shi da mirmushi,'ina tayaka murna ka kusa xama baba,nan kurkusa."me!! ya fada cikin daga murya da bayyana tashin hankali na dirar mikiya mgnr tayi masa,ita kuma ta bada gamm!!! kanta ya bugi bango,tunaninta taxo qofa,'yallabai ko baka son haihuwane?"ya qirqiro mirmishin qarfin hali da kyar daya tuna a gaban wanda yake,a kalla xaifi kowa jin kunyar ya nuna halin bai san da xaman cikin gaban likita ba,yace nikuwa nake sonta,nagode da wannan albishir,'ya sallameshi,ita kuma yabita daki,tana ganinsa ta fashe da kuka,shima sauran qiris yayi kukan sbd tsananin takaici,da kakkausar murya yace,'wayayi maki ciki?tayi shiru ta kasa motsi,ya daka mata tsawa,nace uban wa yayi maki ciki?durqushewa tayi a gabansa,'don Allah ka rufamin asiri,wllhi...'in rufa miki asiri na in amshe shege?tashi kibarmin gida,ya nufi qofa,ta bishi xata riqe masa riga,yayi saurin tsayawa tareda wurga mata wani mugun kallo,kinci sa'an cikin shegen dake jikinki,da wllhi na sake maki yatsu,kuma na baki minti goma sha-biyar,wllhi kika wuce haka da hukuma xan hadaki,yana gama fadin haka yayi ficewarsa.
[6:30pm, 11/7/2016] sadia tahir: *~SAFNAAH~* by billy tabaco~sad-nas
9.......
"mahaifin Abdoul cikakken dan garo ne,wato mahaifarsa kenan,amman cikin kaduna yake da iyalansa dalili kuwer aiki yakaishi chan,mahaifiyar abdoul kuwer yar bichi ce wato kano'Allah yasaka suka xamto inuwa daya,'abdoul shi kadai Allah ya axurta ma iyayensa,'shiyasa suka dauki son duniya suka daura masa,amman duk kudinsu duk son dasuke masa,'basa taba bari yayi abinda xai kaucewa hanya koh addini,'basu reneshi da sangarci ba,'shiyasa ya taso da biyeyya,bin iyaye,girmama babba da bin mgnr babba da son al'umma annabi tausayin marasa qarfi da kuma taimakonsu da abin da Allah ya axurta masa,'gashi ingarman namiji,fari dogo ga hanci gashi da jiki amman irin najin dadinnan bamai yawa ba ga kwala-kwalan idanuwa kaman xasu fado,amman abdoul a duniya Allah,yan mata basu gabanshi.toh bayin Allah masu bina dan taqaitaccen labarin abdoul nnpc kenan kubiyoni muje xuwa.
_dawowa labari_
"fulani ne xalla cikin kauyen,'bbu surki,idan kaga maxa da matan garin kai kace saudiyya kake,bambamcin kawai rashin gyara da wayewa,'mlm muhammdu nasidi,wasu sunfi saninshi da nasidi sbd inkiyarshi kenan mlm nasidi,'shine kusan wandayayi fice a arxiki ciki kauyen,'Allah ya axurceshi da gonaki da shanu masu tarin yawa,'yanada mata uku,rabi suwaiba dakuma rakiya,'rabi nada yara takwas harda rumasa'u wadda suke kai daya da hansa'u yar wajen suwaiba,dakuma baiwar Allah SAFNAAH diyar rakiya.
[6:30pm, 11/7/2016] sadia tahir: *~SAFNAAH~* by billy tabaco~sad-nas
10......
"rakiya taxamo mai hakuri da biyeyya kwarai da gske,'shiyasa mlm nasidi yake matuqar sonta da ya'yanta,domin ta horesu da biyeyya ga duk wani nagaba dasu,suna mutunta mahaifinsu da sauran matan gidadn,sabanin su suwaiba da idanunsu tsaitsaye basu ragwantawa rakiya,'dashi kanshi mai gidan nasu,sun hade mata kai ita da ya'yanta sun ware su,gefe guda.
"abin mamaki,wannan kauyen sai Allah ya albarkacesu da sanya ya'yansu makarantar boko da islamiyya dake chan gaba dasu,karfin a fitar marayar wadda sai anyi tafiya mai nisan gske,yanxu haka su safnaah suna aji shida a matakin secondary,wani abu daya kara haddasa wa safnaah tsana ita da mahaifiyarta da sauran yan uwanta shine,irin qoqarin da take dashi,kullum ita ke dakko na daya,'sannan mahawara(dabate) nd (quise) din da ake xuwa ita ke jagoranta,'wannan karatu dasuke yi bai hana ta talle ba idan sun dawo,'rumasa'u ke saida gyada koh goro,ita kuma wani lokacin ayi mata awara.rannan maraice kwatsam akayi baqi yan birni,cewar anxo ayiwa garin hanya,'da kuma jawo wutar lantarki,"waiyyo murna,'dandali ya cika maxa da mata anata murna da shagulgula,safnaah na gefe sai mirmishi takeyi,shi kuma tun daga nesa ya hango ta,'yaqaraso yana daria.ranki yadade meyasa waikee kullum baki rawa a dandali? ta tsuke fuska rai a bace"a taqaice tace dashi ra'ayi,yaqara mirmishi,yau ka dai ki daure,domin a kece raini,a gane wandayafi sonki tsakanina da mando don Allah,'ganinsu mando,sun nufo wurinsu yasata yi baya kawai,tayi tafiyarta gida.
[6:30pm, 11/7/2016] sadia tahir: *~SAFNAAH~* by billy tabaco~sad-nas
11......
"safnaah kenan,Allah yayi mata farin jinin samari a garin,sbd kyawunta da Allah yabata,da kuma kyawawan dabi'unta.sai dai ita sam yin saurayi ba shine a gabanta ba,kullum burinta tayi ilimi mai tarin yawa,ta ringa shiga birni,"ranar asabar ma'aikata sukaxo don fara gudanar da aikin hanya,don haka ko wacce kokarin gabatar da kai tallarta takeyi,ga wadannan ma'aikatan."ma'aikatane majiya karfi,ko wanne yaxo da himmar aiki,sabanin wani matashi wandaya kasance makure yake gefen hanya,hannunsa rike da takardu,'kallo daya xakayi masa kagane yana cikin damuwa da rashin walwala."kayansa wani iri ga wani baqi da yake dashi mai shuni,hannunsa daya,ga hanci mai tsawo,sai dai m
kuma gashin kansa kwance yake lub-lub-lub bisa kansa."yara da yanmata garin sukayiwa wurin da'ira ana talla,nan kuwa aka far musu da saye,'wanda safnaah na cikin wayanda suke saida nasu da gaggawa ta koma gida da sauri,don qara debo wata awarar,'lokacin data dawo masu motocin sunfara katse hanya,'sauran ma'aikata na xaune,ana harhada sauran kayan aiki,'su hansatu sai wannan feleke sukeyi,'safnaah ta sami wani icce ta xauna a karkashin inuwa,daga nesa da ita saurayin nan ne xaune,'yayi tagumi,wani ma'aikaci ya rufeshi da masifa,nan ma lalacin xakayi mana?wllhi baxamu dauki hakan ba,kanka ba farau hannu daya ba,ko an fada maka xamu dinga wahalane kana kwasar kudi?toh wllhi wannan karon baxamu rufa maka asiri ba,oga xamu sanarwa idan yaxo."yabuga tsaki,yawuce yana faman mita,safnaah taji tausayinsa kwarai da gske,kawai sai ta kasance duk wani motsin bawan Allah nan xaiyi yana kan idonta,'ga wani abu data lura,ma'aikatanan na siyan duk abinda suke buqata amman banda shi,da hannu dayannan yake tura qasa da duk wani aiki qarfi,'amma duk da hakan bbu wanda ke ragwanta masa,kowa ya tsane shi.
[6:30pm, 11/7/2016] sadia tahir: *~SAFNAAH~* by billy tabaco~sad-nas
12.......
"kwana daya,kwana biu kai har kusan kwanaki hudu,bbu abindaya sauya saima gaba yakeyi,'A ranar ta biyar,safnaah ta dibo awara masu xafi,bbu inda ta xarce,sai gurin wannan bawon Allah,nan yake xaune yana faman shirya takardu,'tayi sallama,da sauri ya dago kai,ya amsa a gajarce,'tareda daci gaba da aikinsa."ta tsugunna gabansa sai kawai ya ajiye aikin da yakeyi,'ya kura mata ido yana mamaki,dai-dai lokacin da wata takarda ta ruga iska yafigeta,'ta ajiye bokitin awarar ta kwasa a guje tun karfin ya motsa ta kamo masa,har lokacin da ta miko masa bai daina kallonta ba,ya amsa ta miqa masa tana mirmishin ya kawar da kai,ta dauko leda fara,'ta cika masa da awarar ta xuba masa albasa,sannan ta ajiye gabansa,'karfin yadago kai ya kalleta,har ta juya ta tafi,yabita da kallo yana wani irin mamaki."kamar ita kadai ma'aikatan ke jira,tana isa,aka wawushe wannan ya kara harxuka su hansa'u,suka dauri kudirin yin awarar daga gobe,'su kansu masu aikin suna yabawa da kamun kan safnaah,sannan tana da girmama manya,'inda take gaida kowa sabanin sauran yanmatan."wannan yasa tayi kwarjini sosae a gurin,'shikuwer mai hannu daya,kusan yini yayi yana mamakin wannan yarinya."washe gari tunda safe suka shirya xuwa makaranta,amma hansa'u da ruma suka yaye kansu,'domin ganin cinikin dasuke a tallarsu,ran mlm nasidi yabaci,kwarai amman da yake sun raina mgnrsa ko sauraronsa basuyi ba,'ita kuwa safnaah sai ta taso take xuwa da dare,kuma tayi tafiyarta islamiyyar dare,'wanda su ruma ana dandalin a lokacin,'ta taso karfe biu,ta wuce tana gaishe da kowa,shikuma yana chan yana tura uban qasa a gefen hanya,amma duk da hakan bbu mai kawo masa rangwame,kowa ya tsanesa.
[6:30pm, 11/7/2016] sadia tahir: *~SAFNAAH~* by billy tabaco~sad-nas
13......
"ta karasa kusa dashi,sannu da aiki,'ina yini?ya kalleta,yauwa" _wannan mutumi bashida galihu ta fada cikin ranta_"ta fada cikin ranta."bayan komawarta gida a gurguje tayi wanka,har innarta ta gama mata fura,ta kwashi kayan ta tafi da nono mai kyau,gashi bbu tsami kamar madara.'ya hango tahowarta da kaya niki-niki bisa kaiga wasu a hannu,haka kawai yarinyar mamaki take bashi,tana gama ajiye wa ta nufi inda suke,ta ringa tambayar kowa ta nawa xa'a damo masa,'wacce nono ne kawai bbu ruwa cikinta,ta saka ludayi,ta rufe da dan fai-fai,ta nufi inda yake tsaye yana aiki,ga uwar rana ga wata xunbulelen suwaita da yaje sawa kullum,sai faman xufa yake,tace dashi sannu ya aiki,ta fada a hankali tana mirmishi,da sauri ya waigo dan baigi tahowarta ba,ta miqa masa furar tana mirmishi,ya kalle sosae karfin ya girgixa kai,ta ajiye masa kasa tajuya,yabita da kallo,yau shi yaga takansa,ta koma taci gaba da dama sauran,nan da nan fura yaqe,tabasu lokaci karfin takoma tacigaba da tattaro robobinta,dataje gurinsa,saita tarar bai sha tasa ba,sai ta sunkuya xata dauka ya dakatar da ita,dacewa ki ajiye mini xan maido miki har inda kike,wani kallo tayi masa da sauri tana mamakin taushi da laushi na muryansa,ashe,shiyasa baiyin mgn?Allah yayi masa dadin murya haka?taji dadi yakamata batare da tasan dalili ba,tayi mirmishi sai kawai taga ya maido mata da martani,xaune take tana kirga kudin cinikin datayi,ta karaso,tabi shi da kallo,gskiya bai da tsari na fuska,bakinsa ba mai kyau bane amman yanada natsuwa..
[6:30pm, 11/7/2016] sadia tahir: *~SAFNAAH~* by billy tabaco~sad-nas
14.....
"ya tsugunna gabanta,'gashi ngd ta nawa ce?ba tareda ta kalleshi ba,tace ta kyauta ce,"kyauta?ya maimaita,jiya fa kinbani awara ba'ayi miki fada ne?tana jin dadin sauraron mgnrsa,yana da baiwarta sosae,ta girgixa mai kai,'ae anayi mani dauri gyaran ciki nake baka,meyasa kike saidawa kowa nikuma kike bani kyauta,'ta danyi jim tareda kallonsa,sannan tace,'ganin baka taba sayen komi ba,kuma abokan aikinka basu tausaya maka,suna matsanta maka,'yayi mirmishi,'ko kina tausayinane,kwarai kana bani tausayi,ganin hannunka daya kana aiki irin wannan,dariya yayi,fararen hakoransa suka bayyana,tabi bakin nasa da kallo,ae kuma muna samun kudi dayawa,bakiyi tunanin ra'ayi nane rashin cin abincin naku ba,,?ta sake kallonsa sosae,tace ashe kana da kudi?yayi mirmishi,"kwarai jiya an mana biyan farko,ya xaro dubu a aljihunsa,kinga shaida?tayi yar daria da dimples dinta suka fito,kai amman da wayau kake,mgnr na burgeshi gashi duk inda mutum mai dimple yake birgesa yake,ta hango ma'aikata na nuno su da hannu ana mgn,"to wai kai meyasa bakayin gayu kamar sauran?kullum baka wanki tadan harareshi,a lokacinnan tabashi daria sosae yakasa riqe darian,chan ya kalleta sbd sutura bata gabana yanxu,ta danyi mirmishi,toh menene gabanka a yanxu?yace iyayena da yan uwana don su nake wannan wahalar."ALLAH SARKI" ta langwabar dakai yanayin tausayi.
[6:30pm, 11/7/2016] sadia tahir: *~SAFNAAH~* by billy tabaco~sad-nas
15......
"kema naga ae qawayenki na hantararki,ke kuma meyasa?tadan dara,'yan uwanane ko a gida haka muke,'Allah ya kyauta,ya fada tace amin,naga duk sunyi samari a nan,ke waye naki?ta dan kalleshi chab Allah ya kyauta,daga ganinsu bansan daga ina suke ba,kawai sainayi samartaka dasu,'yaboye mamakinshi na hankalin yarinyar,yace sai kasan mutum xaka so shi?tace ehmana ae bbu wanda nake so duk basuyimin ba,ina da saurayina,yace waye?sunansa sale,ya tafi birni karatu,'lalle kema kinada wayau,ta harhada kayanta,bari kaga na mike,kada yammaci ya riskeni nan,meyasa kike tafia da sauri kullum baki jira dakin gama kike tafia,baki jira kaman sauran,yan uwanki da abokanki tare muke tashi dasu ,tabdi! wallahi bani xama inyi meh?ya kyalkyale da daria,sbd yanayin yarda tayi maganar,ta tura duka kayan cikin kwarya ya taimaka mata ta daura a kai,ya miqo mata galan din ruwanta,toh sai da safe koh?Allah tashemu lfy,tajuya abinta,yabi bayanta da kallo yana mamakin natsuwar yarinyar,hankali,kamala da kamewa."wani abu ya tsikari xuciyar da sauri,nan da yagane abin dake shirin faruwa,nan kuma take gabanshi yafadi,daya tuna halin da yake ciki,(wani haline?).
[6:30pm, 11/7/2016] sadia tahir: *~SAFNAAH~*by billy tabaco~sad-nas
16.....
K'agare yake ya gama tura k'asar saboda matsananciyar rana da ake fama da ita a lokacin, zufa yakeyi sosai kamar wanda aka kwarawa bokitin ruwa. Tun daga nesa ta hangoshi tausayinshi ya kamata,zamanta keda wuya kowa ya aiko a dama masa furar,saboda zafin da akeyi a garin yayi yawa,har wayanda basu damu da furarba ranan sunyi sha'awar shanta. Kasuwa ta bud'e mata nan da nan fura ta k'are har ana nema,tayi hanzarin komawa gida ta k'aro lokacinne ta tarar dashi ya gama yana wanke jikinsa. Wasu kewaye dashi kafin ta k'aro har sun watse,ko kallonta baiyiba ya koma inda ya saba zama a k'ark'ashin inuwa. Tacigaba da damun furarta amma hankalinta gabad'aya yana kanshi,ta rasa dalilin dayasa ta damu da wannan kuchakin mutumin. Tunda yake kishingid'e yake waya harta gama damun furar datayi saura,dama ta ware mulmule hud'u,sannan nononsa daban da yake cikin gora,dan haka ta d'auko sauran kwaryan da batayi amfani dashiba tayi masa kyakkyawan damu sannan ta mik'e ta nufi inda yake tuni ya gama waya. Tayi sallama batare data jira me zaiceba ta 'yamutsa fiska irin na 'yan kauyennan tace da matarka kake waya haka? Yayi murmushi yace ko d'aya ni matata ta rasu tun shekaru uku da suka wuce,safnnah taji gabanta ya fad'i sannan tausayinshi ya sake ninkuwa a zuciyarta tayi saurin tsugunawa
[6:45pm, 11/8/2016] Billy tabaco: *SAFNAAH* by billy tabaco~sad-nas
18......
"nidai yau a koshe nake,"koshi mekaci?tuwo yabata amsa,jinyace tuwo saitayi lakwas,indai tuwon yaci da gske ta tabbatar xai riqe masa ciki,sai dai bata iya banbance tuwon birni dana qauye,"har tamike xata tafi,tace"shin wai kai baka da suna,"yace inadashi mana,"kinason sanine,tace ehman cikin wani yanayi da har saida wani abu ya tsikari xuciyarsa,a takaice kawai yace mata dan alhaji,dan alhaji sunane?kwarai kuwa,dashi kowa ke kirana,"na gsky fa,ta buqata,yace hassan,toh ina hussainin,"yayi daria ya mutu daman shi baixo da raina ba,"kai kuwa Allah ya kyauta maka tafada tare dayin gaba,"duk abindaya faru idan ta koma bata boyewa innarta komi,yauma kamar kullum saidata bata lbrin komi,"ranar litinin da wuri ta tafi makaranta,sbd tana cikin yan(quiz)ita a fannin lissafi take makarantu biyar xasuyi gasar,"taro akayi sosae harda manyan mitane,dakuma ciyaman na rano,"kamar kullum safnaah ita ta lashe masu gasar,"data taka sauran makarantun harda ta private,"ta amsan wa makarantar kyaututtuka harda motar makaranta ciyaman yabasu kyauta wato(school bus),banda kayan makaranta dasauran tarkacen rubutu,"aka umarci babbab baqo ya rufe taro da addu'a wato alh.abdul nnpc wandaya gina makarantar fisabilillahi,"amman sai aka samu aka yatura mataimakinshi ya rufe taron da addu'a yace dasu yana mura aikuwa yasha addu'a saimun sauqi babba da yaro.
[6:58pm, 11/8/2016] Billy tabaco: *SAFNAAH* by billy tabaco~sad-nas
19.....
"tun a hanyarsu ta komawa gida kuwa dawa Allah yahada,"munafuka,ae kina ganewa,"amman kullum baqin ciki baya bari kikoyamun,da yanxu nima hardani,"toh wllhi baxan yarda ba,muje gida.kala batace mata ba har suka isa gida,cikin sa'a suka tarar da babansu ya dawo,baki har kunne ta karasa tana labarta masu abindaya faru,nan da nan innarta tayo waje tana washe baki,shima sai yar daria yake,ruma ta fashe da kuka tana fadin,duk muna fincin safnaah ne,nima da hardani ciki,"wllhi tallahi bbu ruwana haba ya xa'ayi inmaki haka?ahayye nanaye,rabi tayi shewa daga bakin kofa,na ranste da Allah sai dai ayi biu bbu,ko kuma ita ruma a biya mata,mlm ya kalleta rai abace,"waxai biya mata?kai mana!!ta fada rai a bace saidai kabiya mata wllhi ko kuma safara'u ta xauna(bata cemata safnaah sbd dadin sunan duk dan taba sunan take kiranta safara'u) indai ana neman xaman lfy kenan,"jin fitinar tayi yawa yasa takalmin yayi hanyar fita dan bala'i har xaure suka bishi suna balbaleshi da masifa
[9:17am, 11/9/2016] Billy tabaco: *SAFNAAH* by billy tabaco~sad-nas
20.....
"da kyar ta kawo kanta,sbd nauyin da kayan suke dashi,xaune yake a gurin,"yanata faman sana'a wato rubutu.ganinta da kayan yasa shi mikewa da sauri,"yana sauke mata da hannu daya,duk yabata tausayi,tace barshi abinka,wllhi xa'iya saukewa,"karki gwatsaleni mna,har takai gawasu suji suyi mna daria,"ya fada yana mirmishi,tayi yar daria kawai,'yana gama sauke mata yakoma tareda cigaba da rubutunsa,"takura wa takardun idanu,sannan ta kalleshi,gaskiya ka'Iya rubutu mai kyau,"batareda ya kalleta ba yace koh?tace sosai,yayi mirmishi,ngd."tacigabasa da saida furarta,"tanayi tana tambayarsa,"a damo maka?sai yace ba yanxu ba,hartakusan qarewa sauran churi shida,idan an aiko saitace yaqare,yakalleta wannan fa,"takace koh yau baxaka sha furar ba?yace gsky,to mekaci?nidai duk xamanka anan bantaba ganin koda ruwa kasha ba,"toh mekake ci haka yake riqe maka ciki?yayi mirmishi yana mamakin yadda wannan yarinyar ke tuhumarsa a duk lokacin da xata basa fura,"ki qarasa saida wannan saina fada maki."tabdi!! ae saika fadamin idan naji na gamsu saina siyar,"idan kuma ban yarda ba,sai'in dame maka ita duka,"bakiga muna tafia sallaba,'nagani'ta fada,to a can muna da inda muke cin abinci a gurin,tayi daria na yarda.
[9:17am, 11/9/2016] Billy tabaco: *SAFNAAH* by billy tabaco~sad-nas
21.......
"ta dauko baqar leda ta fiddo riguna,jallabiyoyi irin na gwanjo,guda shida sun sha wanki,sai kamshin klin suke yi tace,"ungo ga riguna amma don Allah ka dinga wankesu kada suyi datti irin na jinkinka,"da sauri ya kalleta cike da wani irin mamaki,wayace ki saimin kaya safnaah?yo ni bakace kudinka na marayu bane,"ke waya baki?babana,kasan naciyo kyauta a makaranta,to da aka raba kudin mu ba'a bamu ba da inna sbd makircinsu goggo,ruma taja sharrin wai nayi mata baqin ciki shine da aka raba kudin sukace tunda inada qoqari naciyo agaba,"to daxu daxan fita baba yayi kirana yabani dari biyar nabi ta kasuwar dare nasayo maka rigunan saba'in-saba'in."kowa tsaf amma kullum kai dauda,shiyasa kowa bayason rabarka,sbd bbu abin dake da haske a jikinka sai hakoranka,"ya sunkuyar da kai,"ina yin tsafta,amma baki ganin yanayin aikin da mukeyi,"ta turbune fuska tace,"duk da haka,su meyasa kayansu basu kai naka lalacewa ba,"yayi shiru," xan saka ngd amman gskiya sai baya muntashi daga aiki(shikuwa jibgegiyar suwartar sace bayason cirewa),"tace toh shikenan wayannan ka dinga baiwa almajirai naira goma suna wanke maka,"yace toh,dame-dame kikasamu a kyautar,"kudine na tafia karatu,amma su goggo sun xuge baba,sbd meh? sbd ruma bata samu ba,kasan ita bata maida hankali ga karatu,nikuwa kullum burina nayi ilimi mai xurfi,"amman wllhi baba yace baxan wuce ba,"ya jinjina kai Allah ya kyauta,"ta bishi da amin.
[9:17am, 11/9/2016] Billy tabaco: *SAFNAAH* by billy tabaco~sad-nas
22......
"to amma safnaah kekike ta wahala dani bantaba yimaki kyauta ba,"tayi daria,to menene,"wllhi bbu komai,"nikuwa kinsan wani abu,sai ka fada,"tana faman wanke kokunan da aka sha fura,"daxakiyi min taimako daya,dana roqeki alfarma,"tame? tace lokacin data ajiye kokon tareda maida hankalinta gabadaya gare shi."wanda mukeyiwa wannan aikin,wato maigidanmu kinsan shine wanda yayi maki wannan kyautar,jin inda ya dosa saita xauna sosai,"domin tana tunanin watakila xaiyi mata hanya ne aje a sami babanta akan batun makarantarta."kwarai kuwa ina jimka,"ta fada,xan fada maki amman amana,sai kinyi min alkawari baxaki sanar da kowa ba,ko da kuwa mahaifiyarkice,"tace wllhi nayi alkawari,"yace abinda ke faruwa,"mutum ne mai karamci,mutunci,kyauta da girmama dan Adam,baya kyamar mitane sannan bayada rowa.wllhi safnaah na yaba da hankalinki ,na tabbatar xamu dace da juna,"ya sami matsalar aurarraki,bai taba dacewa da mace tagari ba har yau,gashi anfara masa shaidar baya xama da mace,kudinsa na rudarsa daya auri mace ya gama da ita to sai ya nemi wata."kuma wllhi ba haka bane,"domin shi mutum ne mai addini,"idan har kin amince xanje in sameshi,domin ina daya daga cikin ma'aikatansa wadanda yakeji dasu,kinga wadannan takardun to duk inda mukaje aiki nike da rubutu shiyasa kowa ya tsaneni ana ganin yadda yayi dani gashi dai hannu daya gareni,"xan labarta masa ke idan har xai aureki!!!,"taxaro ido ni!!kwarai kuwa,"A'a wllhi dan alhaji,ni duk abinda nake yimaka sbd Allah ne.....
[1:53pm, 11/10/2016] Billy tabaco: *SAFNAAH*by billy tabaco~sad-nas
23......
"nasani safnaah sai dai.."ni banason wulakanta kaina,"kudi ko kyau basune gabana ba,kullum burina nayi karatu mai xurfi,yadda xan'iya dogaro da kaina,'har in taimaki iyayena da sauran al'umma."a tunani maxaka taimakamin akan wucewata karatune ba wannan batu ba,"shekaran jiya yaganni tunda shine ya bayyana kyaututtuka da kansa,mexai hana yace yana sona ba lokacin,"sbd baisan halinki na kwarai ba daya sani bbu abinda xaya hanashi,"kamar yadda kike da kyau ya auri kyakyawa,"kuma suka cutar dashi,kuma idan naje xanje baxan nuna masa akan munyi mgn ba,kawai xanje masa akan ra'ayi nane,"tace hummm,"kin amince inji dan alhaji kenan,"ni wllhi ma inada wanda nakeso ya tafi birni karatu,"tun ina karama mukayi alkawari,kuma har yanxu yana aiko min da gaisuwa,"kinfadamin shi kuma na tambayi su ibro sunce tuntuni yayi aure,"dan har ya kwashe iyayensa ya maidasu birni,"karya suke chan makarantarsu ya maidasu,"baisan san lokacin daya sake daria ba,'kagani duk ka shagalartar dani xan makara,"tamike tana harda hada kayanta,"yace toh yanxu ina muka tsaya kina gani nayi masa mgn bbu matsala,"tafigi kayan ta duk yarda kagani.
[1:53pm, 11/10/2016] Billy tabaco: *SAFNAAH* by billy tabaco~sad-nas
24.......
"washe gari ,"waiyau rowar fura akemin,"amma kai a gaisheka da neman mgn,"kullum sai nayi maka tayin furar baka sha,"sai dameta ko kuma na nuna banji dadi ba sannan kake sha,"yayi mirmishi kawai,"Af! kinga na mance da mgnr jiya fa,amma bari nakira shi,ga mamaki saiya bude (handfree),"yanayin muryarshi saitaji wani iri,"dan Allah yafishi laushin murya bbu hadi,"mai gida dama wllhi a inda muke aikin nan naga wata yarinya mai hankali da nutsuwa,"shine nace ko xaka jaraba aurenta domin ta fito daga gidan mutunci,itace ma kaje makarantarsu kwanaki uku dasuka wuce,"tana cikin wadanda kabaiwa kyauta."sandaya gama sannan yace"kai dakata dan alhaji,banason shishigi lalle ka tsaya matsayinka,tun karfin ranka yabaci,"ashe duk daukar danake maka,"kaima takai dakai xa'a hada baki a cuceni,"na ranste da Allah mai gida...."rantsuwarka ta banxa da wofi,idan har da gske diyar kwarai ce ka aureta mana,ko kai matar gareka,"idan kun dawo komi dare kasameni a gida,"ya qarashe mgnr da jan tsaki,sha-sha-sha kawai."ya katse wayar,"tuni safnaah ta sandare inda take wannan wulakanci dame yayi kama,"shikuwa tunda ya sunkuyar dakai yakasa dagowa kunya ta lullubeshi,"safnaah kuwa ta figi kayanta tayi gida..
[1:53pm, 11/10/2016] Billy tabaco: *SAFNAAH* by billy tabaco~sad-nas
25......
"kuna ina,bakowa ne,"wai duk mekukeyi a daki kunyi shiru haka,"ya fada a harxuke cikin daga murya,suwaiba tafara jiyo shi tafito,"mlm lfy kaketa hayaniya kai kadai a tsakar gida,"au haniya nakeyi mako,"ya fada yana mai hararta,ta gyatsine baki,"kayi kai kadai wllhi dan banina kashe xomon ba,"haka kawai anbato maka rai a waje xakaxo ka huce a kanmu,"ta leka dakin rabi yaya!yaya!! lokacin da rakiya ma tafito daga bandaki da buta a hannunta."ina ta gyaran murya mlm a bandaki baka jiyoni ba,"to kilibabbiya,yar na'iya gidan uban wa kikayi masa wani gyaran murya,rabi ta fada a hasale,"mu muna jinsa mukayi shiru kome kike nufi,"ke dakata rabi,banason neman fitina,yanxu haka ban kashe wadda kuka ruro minba gurin mai gari,ta kwalo ido mai gari kuma mlm damukayi meh,yanxu xan sanar daku domin sako yabani nabaku...mgnr xuwa makarantar yar baba ne,yace lallai ace maku bbu fashi,baxaku maidashi mutumin banxa ba,"an xabi yar kamar kayan kungurmi,shine xamu bashi kunya tunda mu bamu da ita."haka inji rabi(ladingo),idan ma wani munafircin kake shirin kullawa ka warwareshi,don kuwa safara'u batta xuwa birni tabar ruma."shikenan xan bada rabi,saikiyi koqari ki hado rabi mukaita,"eh xan bayar,naji ehee....ganin mlm yayi hanyar fita wuf tayi daki kar abin yakoma kanta,"amman duk da haka sanda aka bita da kalmar munafuka.
[7:26pm, 11/10/2016] Billy tabaco: *SAFNAAH* by billy tabaco~sad-nas
26.....
"washe gari kenan,"dan Allah yau bakada lfy ne, na ganka haka kwance tun daxu,"lfyta qalau safnaah,wllhi yanayin ne na yau sai a hankali kinsan jiki da jini,"tayi murmishi,tace lallai kam,yauwa jiya yakukayi da maigidanka,"ya korata xaiyi,yanxu haka ina jiran takardar sallamane,don har nayi wa mlm musa wani abokin aikinmu mgn xai saimin keke napep na dinga haya,"ta dafe qirji inalillahi wa'in ilaihir raju'un,meyayi xafi haka don Allah,"amman wannan mutumin bashi da imani,don Allah kaje ka bashi hakuri,keke napep mai hannuwa duka ya yaqare balle kai me hannu guda dan alhaji,"hmm wllhi baxai taba saurarata ba,domin mgn daya yakeyi."ta rushe da kuka,duk laifinane,don me xaka kawo shawarar da baxata taba amfaninka ba,"shawarar da xata rushe duk wani farin ciki dakake fama dashi,"ta kalleshi sosai,"ina ne gidansa?da sauri ya dago yana dubanta,"mekike nufi,xamu je da baba mu rokeshi yabarka a karkashinsa,ya girgixa kai,"karki kuskura koda wasa dan xamu fuskan hukunci mai muni,kamar meh fa,"kamar dai yadda kikaji nafada,"kukan da take yaqaru,"daya daga cikin ma'aikan suka gani a gabansu,ganinsa da leda tare da farar takarda ya maida hankalinsa gurin,"ga wannan"yamiqawa dan alhaji tarkardar(ya kara miqa masa leda)sallamace inji oga,"har yajuya sai yadawo,don Allah dan alhaji wani laifi kayiwa oga yamaka haka,a yadda ya daukeka.
[7:26pm, 11/10/2016] Billy tabaco: *SAFNAAH* by billy tabaco~sad-nas
27......
"yayi mirmishi yace katsalanda,"to Allah ya kyauta,yayi wucewarsa kawai,"ta hada kai da gwiwa sai sharban kuka take,tarasa meyasa take tausayawa dan alhaji matuqa har xuci,"kinga tafia xanyi amman dole nabiki gida,domin na musu bayanin kukannan,karna bar baya da qura,"haka yadiban mata wasu har gida,"cikin sa'a suna isa baba kuma yafito daga gida da shirin tafia kasuwa,"yar baba ya akayi,"lfy daiko saita fashe masa dakuka,"ya kalli dan alhaji a tuhumance mlm yadai,ya durkusa cikin girmamawa suka gaisa,amma shi mlm din gabansa nata faduwa,"ya kwashe tun daga ranar dasukaxo har yau bai boye wa mlm ba komi ba,"kasa rufe baki yayi ya fara fadin,inalillahi wa'in ilaihir raju'un,"ita kawai yake maimaitawa,ae dole yar baba tayi kuka dannan,"subhanallahi dawo nan yaro.'ya fada tare da matsawa chan karkashin inuwar bedi dake gefen gidan,"baba kada hankalinku ya tashi,mu dauka ko da wannan ko ba wannan lokacin barin aikinane yayi."haba yaro ae dole hankalina ya tashi,"duk wanda ya kalle ka yasan kana buqatar taimako,"dan alhaji yace,yanxu haka ni farin ciki nakeyi,domin dama inason sauya sana'a,bani da kwarjini gurin abokan aikina,Allah ya taimakeni,yabani jari wanda xan kafa sana'ata ni kadai ba kwaba balle hantara,mlm nasidi yayi jim yana sauraronsa,chan ya dauko wata leda aljihun shi ya warware ta...
[7:26pm, 11/10/2016] Billy tabaco: *SAFNAAH* by billy tabaco~sad-nas
28......
"dubu dubu ne,daddaure har biyar,ga mamakinsu sai sukaga yana daria mai dauke da farin ciki,ya daga hannu sama masha-ALLAH kaga baba dubu dari biyar yabani,"mln nasidi yayi qasa da murya yanxu yaro karfi murnar wannan kudi akan aikinka,"sosae baba don nadade ina nemansu domin ingujewa aikin wannan tura kasar dan duk inda mukaje aiki tura kasa ake ban,"kuma akwai motar da akeyin hakan amman ni dole sainayi,"safnaah tayi kasa da kai,toh yanxu ina xaka tafi,a takaice yace mata kaduna xan koma na nemi aikin yi,"to yaro Allah ya taimaka,amman shawarata ni kasami sana'ar xaune,kasancewarka mai hannu daya,insha Allahu baba xan duba,nagode kwarai,sannan ina neman alfarmaku sbd ni ne nakai kararku gurin maigari a tafia makarantar safnaah,murmishi yayi Allah sarki amman naji dadi,Allah yayi maka albarka,bbu komi ni kaina inason tayi karatun,"idan bbu damuwa baba xan ringa xagayowa muna gaisawa,"daga kenan yaro,badai kaduna ba ko,lalle jarin naka xai kare gurin xiyartarmu,"haba baba,ae xumunci ne watakila ta dalilin xiyartarku sai jarin yaqaru,mln nasidi yakura masa ido yana yaba hankali irin nasa,"toh shikenan,Allah yabada iko ni xan wuce kasuwa,"gashi baba baka sanyawa kudin nawa albarka ba,yace Allah albarkacesu ya hada fuskokinmu nan gaba yaro ina maka fatan alkhairi bissalam mlm yayi wucewarsa kasuwa.
https://mynovels.com.ng/jiki-na-yake-so-complete-hausa-novel/
ReplyDelete